(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, masana kan harkokin magunguna da kuma kwararru kan kwayoyin cuta a Hong Kong sun gudanar da aiki na hadin gwiwa, inda suka samar da wani magani, wanda ya aka jarraba shi kan masu cutar corona, kuma ya kashe dukkanin kwayoyin cutar da ke cikin jikinsu.
Bayanin ya ce an samar da maganin ne ta hanyar hada magunguna daban-daban da suke kashe kwayoyin cuta, da kuma wasyu magunguna masu kara karfin karkuwar jiki.
Bayanin ya kara da cewa, an gudanar da gwajin maganin a halin yanzu a kan mutane 12 wadanda dukkaninsu suna dauke da kwayoyin cutar, amma yanayinsu bai kai gargara ba, kuma sun warke bayan shan maganin.
Masanan sun ce za su ci gaba da gudanar da aikinsu, tare da fadada aikin ta yadda zai zama na hadin gwiwa tsakaninsu da sauran masana na duniya.
/129
10 Mayu 2020 - 05:17
Lambar labari: 1035214
Wasu masana a Hong Kong sun sanar da samar da wani magani da suka hada da ke kashe kwayoyin cutar corona.